PROGRESS RADIO 97.3 FM Gombe

  Yanci da Cigaban Al'umma 

News

An daura auren zaurawa sama da 1,000 a Kano

Posted by Admin on February 26, 2017 at 11:40 AM Comments comments (0)

-Gwamna Ganduje ya jagorancin daurin auren zaurawa sama da 150,20 a Kano

 

-A yau ne aka yi taron daurawa zaurawa sama da 1,502. aure a jihar Kano a karkashin hukumar Hisbah

 

-Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba sarkin Kano ne suka jagoranci taron daurin auren da aka yi babban masallacin Juma'a na cikin birnin Kano da kuma kananan hukumomi na 44

A yau ne 26 ga watan Fabarairu shekarar 2017 aka daurawa zaurawa sama da 1,000 aure a jihar Kano a karkashin hukumar Hisabah.

 

 

Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje da Mai martaba sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi na II ne su ka jagoranci daurin auren da aka yi babban masallachin Juma'a na mai Martaba Sarki da ke cikin birni.

 

An dai karkasa daurin auren ne zuwa manyan masallatan juma'a 4 na cikin kwaryar birnin inda mataimakin gwamna Hafiza Abubakar, da kakakin majalisar dokokin jihar, da kuma shugaban hukumar Hisbah su ka jagoranta.

 

An kuma karkasa sauran wurararen daurin sauran zuwa kananan hukumomi 44 na jihar a inda aka gudanar a masallatan Juma'ar shalkwatar kananan hukumomin.

 

An kuma gudanar walima a gidan gwamnatin jihar Kano inda malamai suka yiwa ma'auratan liyafa tare da wa'azi kan muhimmancin aure.

 

Ga hotunan daurin auren da aka yi da babban masallacin Juma'a na cikin birni

 

Gwamnatin jihar ta shirya bayar da sadakin Naira 20,000 sadaki ga amaren tare da kayan daki.