PROGRESS RADIO 97.3 FM Gombe

  Yanci da Cigaban Al'umma 

News

Labarun Hausa

Posted by Admin on February 27, 2017 at 10:20 AM

A CIGABA DA KASANCEWA DA TASHAR YANCI

PROGRESS RADIO 97.3 FM GOMBE

INDA ZAMU ANTAYO MUKU LABARUN DUNIYA A HARSHEN HAUSA TARE DA HASSAN LAWAN KOLI

KANO

Gwamnatin jihar Kano ta aurar da zawarawa mata da maza sama da 1,500 a karshen mako.

Gwamnatin jihar ce ta dauki nauyi aurar da mutanen a wani yunkuri na ragewa iyayen da ba su da karfin aurar da 'ya'yan su hidima, da kuma rage yawan marasa aure a jihar.

Ba wannan ne karon farko da gwamnatin jihar Kano ta fara aurar da zawarawan ba, an faro wannan aikin ne tun zamanin tsohon gwamnan jihar wato Injiniya Rabi'u Musa Kwankwaso.

A wannan karo an zabo sama da mata da maza talatin a kowacce karamar hukuma da ke jihar, wanda kuma gwamnati ita ce ta biya kudin sadaki da kuma sanyan kayan daki ga ma'auratan.

An gudanar da daurin auren ne bayan da aka tantance ma'auratan ta bangaren lafiyar jikinsu da kuma hankalin su baki daya.

Wannan lamari dai na irin dauren wannan aure na sa matasa su natsu kuma ya kare su da yin zinace-zinace.

GOMBE

Rundunar Sojin Najeriya ta sanar da kame wasu ‘yan kasar Chadi uku da take zargi da shirya kai harin bama-bamai a garin Gombe.

Daraktan yada labaran rundunar sojin kasa na najeriya brigadiya Janar Sani Usman Kukasheka, ya ce sun yi nasarar kama mutanen uku ne tare da rundunar ‘yan Sandan farin kaya ta DSS, kuma sun fito ne daga bangaren Albarnawi, daya daga cikin jagororin kungiyar Boko Haram.

Daraktan ya bayyana sunayen mutanen da suka hada da Bilal Muhammed Umar da Bashir Muhammed da kuma Muhammad Maigari Abubakar.

Lokacin samamen da rundunar sojin ta kai daya daga cikin yan kungiyar ta Boko haram mai suna Bilal Muhammed ya yi kokarin tserewa yayin da rundunar sojin ta harbe shi a kafa, wanda yanzu haka yake karban magani.

Mutanen da ake zargin an kama su ne da bama-bamai wanda yanzu haka ake gudanar da bincike a kan su.

GOV/BENUE

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta yi awun gaba da tsohon gwamnan jihar Benue Gabriel Suswan jiya lahadi a gidansa dake Abuja, bisa zrginsa da mallakar makamai, da filaye da kuma wasu motocin alfarma ba bisa ka’ida ba.

Gabriel Suswan jigo ne a jam’iyar PDP, kuma tsohon dan majalisar wakilai ta tarayya kana ya taba rike mukamin gwamnan jihar ta Benue sau biyu.

Makaman da hukumar ta DSS ta chafke a gidan tsohon gwamnan sun hada da karamar bindiga mai suna pistol guda, da bindiga Mini-Uzi guda, da kuma bindiga kirar AK47 guda tare da tarin albarusai.

Wata sanarwa da jami’in yada labaran hukumar Toyin Opuiyo ya fitar ya bayyana cewa sun samu wasu muhimman takardu guda 21 da kuma makullai guda 45 na motocin alfarma da aka samu a gidan tsohon gwamnan Gabriel Suswan.

SSASCGOC

Kungiyar manyan jami’an jam’iyun gama kai da kuma ma’aikatan kamfanoni mallakin gwamnati sun bukaci gwamnatin tarayya data sanya kudaden da aka kwato daga hannu barayin gwamnati a bangaren bunkasa tattalin arzikin najeriya.

Hakan na kunshe ne a cikin takardar bayan taron da kungiyar ta gudanar a Abeokuta, dauke da sa hannu shugaban kungiyar Muhammad Yunusa da kuma sakatarensa M.O Abogonye.

Kungiyar ta bayyana cewa in har gwamnati ta sanya kudaden a bangaren bunkasa tattalin arziki, to hakan zai farfodo da tattalin arzikin kamar yadda ya dace.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati data yi la’akari da yadda mutane ke rasa aiyukansu da kuma wadan da ke fuskantar rasa aiyukansu a kasarnan.

LABORATORY

Kungiyar masu gudanar da bincike a dakunan kimiyya ta kasa, sun nuna goyon bayan su ga yunkurin yaki da cutar zabbabin cizon sauro a kasarnan.

Mambobin kungiyar sun nuna goyon bayan ne a karshen mako lokacin taron kungiyar na shekara ta 2017 wanda ya gudana a jihar Delta.

Sun bayyana cewa cutar zabbabin cizon sauro na barazana ga kashi 97 na yan najeriya, wanda hakan ke janyo rasa rayuka dubu 300 a kowacce shekara a fadin najeriya.

Mambobin kugiyar ta masu gudanar da bincike a dakunan kimiyyar sun bayyana cewa wannan lokacin ne na waywayar halin da dakunan binciken kimiyya na asibitocin kasarnan ke ciki, don ganin an ingatasu ta yadda zasu rinka aiki kamar yadda ya dace.

A KARSHE

Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce 'yan kasar Sudan ta kudu dubu 32,000 suka shiga kasar Sudan a cikin wannan shekara kawai, dan tserewa tashin hankali da kuma yunwar da ya dabaibaye kasar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin kasar ta bayyana cewar mutane sama da 100,000 na fuskantar tsananin yunwa a kasar.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce hasashen ta na da, ya nuna mata cewar mutane 60,000 ake saran za su shiga Sudan a wannan shekara, amma adadin da aka samu yanzu haka ya nuna cewar ba haka abin yake ba.

Hukumar tace ana fargabar tabarbarewar al’amura wajen samun abincin da za’a ci a Sudan ta kudu ganin yadda tuni aka bayyana samun yunwa a kasar.

Sanarwar hukumar ta nuna cewar, wasu daga cikin yan gudun hijirar sun ce sun kwashe kwanaki 5 zuwa 7 suna takawa da kafafuwan su dan isa iyakar Sudan ta Jihar White Nile, kuma kashi 90 na bakin mata ne da yara kanana.

Hukumar tace yanzu haka yan sudan ta kudu 330,000 suka shiga Sudan tun fara yakin kasar.

A SAURAREMU A KAN MITA 97.3 FM GOMBE

A TUNEIN RADIO KO TUNEIN APP http://tun.in/sfqot

SANNAN A YANAR GIZO www.radio-progress.com

Categories: International, Business, Economy

Post a Comment

Oops!

Oops, you forgot something.

Oops!

The words you entered did not match the given text. Please try again.

Already a member? Sign In

1 Comment

Reply Abdullahi telan yen'agaji
5:50 AM on August 9, 2017 
Allah yakaramaku basira lallai kunchika tashar yenchi